Labarai
Antoni janar da wasu manyan gwamnatin na kasar Burtaniya don bude shari’ar Kamfanin P&ID
Attorney Janar na kasa kuma Ministan shari’a Abubakar Malami da sufeto Janar na ‘yan sandan kasar nan Muhammed Adamu da gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefiele, sun tafi kasar Burtaniya domin sake bude sabuwar shari’a da kamfanin P&ID wanda wata kotun kasuwanci ta Burtaniya ta ba ta umarnin kwace kadarorin kasar nan da suka kai darajar dala biliyan tara da miliyan dari shida.
Haka zalika Ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammed da kuma mai rikon mukamin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Ibrahim Magu, suna cikin tawagar da su ka tafi burtaniya.
A dai watan jiya na Agusta ne wata kotun kasuwanci da ke Burtaniya ta yanke hukuncin cewa kamfanin P&ID yana da hurumin kwace kadarorin kasar nan a duk inda ya same su da darajarsu suka kai sama da dala biliyan tara sakamakon zargin hukumomin kasar nan da karya kai’don kwangilar harkar gas.
Bayan yanke hukuncin ne a watan jiya ministar kudi, kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed , ta bayyana hukuncin a matsayin marar adalci kuma kasar nan ba za ta amince da hakan ba