Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta lalata kwalaben barasa 196,400

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta lalata kwalaben barasa sama da dubu dari da casa’in da shida da dari hudu, wanda ta kama a wasu sassa na birnin Kano.

Wannan na dauke cikin sanarwar da babban sakataren yada labarai ga mataimakin gwamnan jihar Kano Hassan Musa Fagge ya fitar.

Da yake jawabi jim kadan bayan lalata kwalaben a yankin Kalemawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa, gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yace addinin musulunci ya haramata shan giya ga duk wani nau’in abubuwan dake sanya maye, ko gusar da hankalin dan adam, a don haka ya zama wajibi hukumar ta Hisbah ta lalata kwalaban.

Abdullhai Umar Ganduje yayi bayanin cewar addinin Isalam yayi hani da shan miyagun kwayoyin da ke gusar da hankali, tare da kira ga malaman addinai da su hada hannnu  wajen yaki da shaye-shaye a jihar Kano.

Gwamnan na Kano wanda ya sami wakilcin mataimakin sa Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna ya baiwa hukumomin shari’a na jihar nan tabbacin goyan bayan gwamnati wajen yake da sha da miyagun kwayoyi mussaman ma shan barasa.

A cewar sanarwar mataimakin gwamnan ya kara da cewar gwamantin Kano zata cigaba da tallafawa hukumar Hisbah mussaman bayan da aka kamala kaddamar da kwamandojin kananan hukumomi 44 na jihar nan.

Da yake jawabi babban kwamandan Hisbah na jihar Kano Sheik Haruna Ibini-Sina, ya hukumar ta ci nasarar hana saida barasa da shan sa a cikin birnin Kano da kewaye, karkashin sashi na 401 na kudin tsarin shari’ar musulunci na nan Kano.

Ya kara da cewar, hukumar ta karbi umarnin kotu na lalalta fiye da kwalaban barasa na motoci 12.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!