Connect with us

Labaran Kano

Anyi jana’izar marigayi Hassan Dalhatu

Published

on

A yau Lahadi ne aka gudanar da jana’izar marigayi Alhaji Hassan Dalhatu wanda ya rasu a daren Asabar da ta gabata.

Alhaji Hassan Dalhatu daya ne daga cikin daraktoci na hukumar rukunin tashoshin Freedom Rediyo.

Anyi jana’izar marigayin da misalin karfe 11:30 na safe a gidan sa dake titin Yusuf Kwari, a unguwar Badawa Layout kusa da Sardauna Crescent

Marigayin ya rasu ya bar mahaifiyar sa da mace daya da ‘ya’ya uku da kuma ‘yan uwa da dama.

A cikin ‘yan uwan marigayin akwai Alhaji Ado Muhammad shugaban hukumar daraktocin Freedom Rediyo, da Alhaji Bashir Dalhatu Wazirin Dutse da Kuma Alhaji Bello Misudan Tafidan Dutse, da kuma ‘Yan dakan Kano Alhaji Abbas Dalhatu kuma shugaban rukunin tashohin Freedom Rediyo.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!