Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Motar Dangote ta hallaka mutane a Kano

Published

on

Wata motar Siminitin Dangote ta hallaka mutane hudu a unguwar Gaida da ke nan birnin Kano.

Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito mana cewa, lamarin ya rutsa da wani magidanci mai suna Muhammad Sagir mai shekaru 40 tare da matarsa da ‘ya’yansa uku wadanda suke tafiya akan babur lokacin da al’amarin ya faru.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da Freedom Radio faruwar al’amarin inda ya ce, ‘yan sanda sun kwashi mutane biyar da hatsarin ya rutsa da su zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad.

Sai dai magidancin da matarsa da ‘ya’yan sa biyu sun rasu, yayin da daya daga cikin ‘ya’yan mutumin ya tsira da ransa.

Sai dai DSP. Abdullahi Kiyawa ya ce tuni ‘yan sanda suka cafke motar Dangoten sannan suna cigaba da bincike domin cafke direban motar wanda ya tsere bayan faruwar lamarin.

Karin labarai:

Yan bindiga sun hallaka mutane a Kano

Masu tseren doki sun hallaka wani matashi a Kano

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!