Labarai
APC ta bayyana ranar gudanar da taron Kwamitin Zartaswarta

Jam’iyyar APC, mai mulki ta bayyana cewa za ta gudanar da taron Kwamitin Zartaswarta na Kasa NEC a ranar 24 ga watan nan da muke ciki na Yuli, domin zaɓen wanda zai maye gurbin tsohon Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
jam’iyyar, ta bayyana hakanne ta cikin wata sanarwa da ta fito daga Mataimakin Sakatarenta na ƙasa Festus Fuanter, bayan kammala taron Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar NWC karo na 174.
Festus Fuanter ya ƙara da cewa an riga an aika takardar sanarwar taron zuwa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta INEC, kamar yadda doka ta tanada.
A cewar jam’iyyar, taron kwamitin zartaswar zai mayar da hankali kan cike gurbin shugaban jam’iyyar, wanda ya zama wajibi sakamakon saukar Dakta Ganduje daga wannan matsayi.
You must be logged in to post a comment Login