Siyasa
APC ta zabi sabbin shugabannin ta na kasa

Jam’iyyar APC mai mulkin kasa ta zabi sabbin shugabanninta na kasa a taron da ta gudanar a Eagle Square da ke babban birnin tarayya Abuja inda Farfesa Nentawe Yilwatda ya zama sabon Shugaban jam’iyyar, yayin da Sanata Surajudeen Basiru ya zama Sakataren ta kasa.
Sauran mukaman da aka cike sun hada da mataimakan shugabanni na Arewa da Kudu, sakatare da mataimakinsa, mai kula da harkokin kudi, mai tsare-tsare, da kakakin jam’iyya da sauransu. Haka kuma an zabi shugabannin mata, matasa da masu bukata ta musamman.
Manyan jagororin jam’iyyar sun halarci taron, ciki har da Shugaba Bola Tinubu, Mataimakin Shugaba Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, tare da wakilai daga sassa daban-daban na kasa.
You must be logged in to post a comment Login