Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

APC: Yan Najeriya sun yi farar dabara wajen zaban Shugaba Buhari

Published

on

Jagoran jam’iyyar APC na kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce, al’ummar kasar nan sun yi farar dabara wajen baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari daman zarcewa a karo na biyu ta hanyar sake zaben sa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sa da aka fitar jiya Laraba.

Sanarwar ta ruwaito Tinubu na cewa zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata yana daya daga cikin zabuka mafi nagartar da inganci da aka taba gani a tarihin kasar nan.

A cewar Bola Tinubu al’ummar kasar nan sun ga nagartar shugaba Buhari shi yasa suka sake amincewa da ya zarce a karo na biyu.

Jagoran jam’iyyar APC ta cikin sanarwar ya ce, yana da kwarin gwiwa shugaba Buhari zai bai wa marada kunya wajen kai kasar nan ga tudun mun tsira.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!