Labaran Wasanni
Arsenal ta yi rashin nasara a hannun Manchester City
Bayan dawowa, gasar firimiyar kasar Ingila, sakamakon tsaikon da ta samu akan cutar Corona tun watan Maris kungiyar Arsenal, ta fara gasar da koma baya, bayan ta sha duka a hannun Manchester City.
Wasan wanda ya gudana a yau, Raheem Sterling ne ya fara saka Manchester City a gaba a minti na 45, ana dab da za a tafi hutun rabin lokaci.
Ya yinda jim kadan bayan dawowa, dan wasan Arsenal David Luiz, ya samu katin kora na ja, a minti 49, sakamakon kayar da Riyard Mahrez a cikin da’ira ta 18, an kuma karawa Arsenal kwallo ta biyu a minti na 51, ta bugun daga kai sai mai tsaron gida da Kevin De Bruyne yayi sakamakon ketar da David Luiz yayi.
Kwallo ta uku, matashin dan wasa Phil Foden ne ya zura ta a minti na 90 ana dab da a tashi wasa.
Arsenal na dakon nasarar ta ta farko bayan dawowa daga hutun, ya yin da zata karbi bakuncin Brighton and Hove Albion, ya yin da Manchester City zata karbi bakuncin Burnley.
You must be logged in to post a comment Login