Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

ASUU : Ba ma goyon bayan sayar da otel din Daula – KUST

Published

on

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa reshen jami’ar kimiyya da fasaha ta Wudil “KUST” ta bayyana bakin cikin ta kan matakin da gwamnatin Kano ta dauka na sayar da cibiyar nazarin ayyukan bude idanu na jami’ar wanda aka fi sa ni da Daula.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin jihar Kano da ta sake nazartar kudurin sayar da otel din don samun kyakyawar matsaya.

Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Kwamared Muhammad Sani Gaya ya sanyawa hannu aka raba ga manema labarai.

Hakan ya biyo bayan wani zama na musamman da kungiyar malaman makarantar ta gudanar a ranar Laraba 5 ga watan Agusta.

Kungiyar tace tayi baza ta amince da kudirin na gwamnatin Kano na son chefanar da tsohon Hotal din na Daula mallakin jami’ar ta Wudil.

Ta cikin Sanarwar ta bayyana cewa, tsohon Hotol din Daula mallakin jami’ar ta KUST ne, kuma ana amfani da shi wajen gudanar da kwasa-kwasai da makarantar ke yi, da suka hadar da IJMB dana Diploma da kuma na share fagen shiga manyan makarantu.

Sanarwar ta kara da cewa, majalisar dattawa ta jami’ar ta amince da a fara gudanar da karatun da ba na yau da kullum ba wato “Part Time Degree” a shekara mai kamawa ta 2021 a cikin ginin na tsohon hotal din Daula.

Kazalika sanarwar ta ja hankalin gwamnatin jihar Kano, da kada ta chefanar da gurin, la’akari da yadda makarantar ke kara bunkasa kwasa-kwasan da take gabatar wa a cikin ginin tare da kirkirar wasu sabbi.

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!