Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano ta dawo ta 8 a yawan masu Corona a Najeriya

Published

on

Jihar Kano ta dawo mataki na 8 daga mataki na 7 na yawan masu dauke da cutar Corona a kasar nan.

Hakan na cikin sanarwar da cibiyar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC ta fitar a daren jiya Alhamis, ta shafinta na Twitter, inda ta ce an samu karin mutane 373 da suka kamu da corona a jihohi 19 na kasar nan da birnin tarayya Abuja.

NCDC ta ce zuwa yau Jumu’a adadin wadanda suka kamu da cutar a fadin kasar nan sun kai, 48,116, yayin da aka sallami mutane 34,309 da suka warke.

Haka kuma cutar ta hallaka mutane 966 a sassa daban-daban na kasar nan.

A nan Kano dai, ma’aikatar lafiya ta jiha ta sanar a shafinta na Twitter cewa mutane 17 ne suka kamu da cutar a jiya Alhamis cikin mutane 639 da aka yiwa gwajin cutar.

Mutane 1,661 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a nan Kano, 1,320 daga ciki sun warke, sai mutane 54 da cutar ta yi ajalinsu.

A jihar Kaduna ma gwamnatin jihar ta sanar a shafinta na Twitter cewa mutane 21 ne suka warke daga Corona a jiya Alhamis, yayin da aka samu mutane 40 dauke da cutar cikin mutane 165 da aka yiwa gwaji.

Mutane 1,706 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a Kaduna, 1,493 daga ciki sun warke, sai mutane 12 da cutar ta hallaka a jihar.

A nahiyar Africa baki daya, kididdigar shafin World Meter a yau Jumu’a ya ce mutane 1,088,338 ne suka kamu da Corona, mutum 783,579 daga ciki sun warke, sai mutane 24,724 da suka rasa ransu sanadiyyar cutar a nahiyar.

Ya zuwa yanzu, masu Corona 280,035 ne suka rage wadanda ke jiyyar cutar a sassan nahiyar ta Africa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!