Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Astrazeneca: An tsawaita wa’adin rigakafin corona kason farko

Published

on

Gwamnatin tarayya ta tsawaita wa’adin yin rigakafin cutar corona zuwa makwanni biyu masu zuwa.

Wannan dai ya biyo bayan bukatar da ‘yan Najeriya ke yin a karbar rigakafin kashin farko.

Tun da fari dai gwamnatin tarayya ta sanya ranar yau ta zamo ranar da za a rufe yin rigakfin cutar kashin farko, wanda a yanzu haka an yiwa yan Najeriya kimanin miliyan daya da dubu dari biyar allurar rigakafin.

Shugaban hukumar lafiya a matakin farko na kasa Dr. Faisal Shuaib ne ya bayyana hakan lokacin da yake bada jawabi kan matakin yan Najeriya ga me da rigakafin corona.

Dr. Faisal Shuaib ya ce, hukumar su za ta yi aiki da hukumomin da ke yaki da ayyukan cin hanci da rashawa wajen bankado wadanda suka karbi shaidar rigakafin ta karya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!