Connect with us

Addini

Ku rika taimakawa marasa galihu a lokacin azumi – Buhari ga masu hannu da shuni

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ta ya al’ummar musulmin Najeriya murnar fara azumin watan Ramadan da aka fara a yau talata.

A cikin wani sako da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar a madadin shugaban kasa, ya kuma yi addu’ar Allah ya karbi ibadun al’ummar musulmi da kuma kara hadin kai da zaman lafiya da ci gaban Najeriya.

Sakon ya kuma bukaci al’ummar musulmi da su kasance masu juriya da hakuri da kuma yin watsi da duk wani al’amari da zai janyo rugujewar kasar nan.

Haka zalika a cewar Garba Shehu shugaban kasar ya kuma bukaci masu hannu da shuni da su rika tallafawa marasa galihu musamman wadanda ke rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv

Now Streaming

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!