Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Ta’addanci: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 2 a Kaduna

Published

on

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Wawan Rafi da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna tare da kashe mutane biyu da safiyar jiya Litinin.

Kazalika ‘yan bindigar sun kone gidaje bakwai da mota daya tare da babur yayin harin.

Wannan dai na cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin Gida Samuel Aruwan ya fitar.

Ta cikin sanarwar Aruwan ya bayyana sunayen mutanen biyu da aka kashe da suka hadar Joshua Dauda da dansa mai shekaru bakwai Philip Dauda.

A cewar sanarwar tuni jami’an sintirin suka fatattaki mahaharn lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa daji, sai dai sojoji sun yi nasarar kwato wasu akwatuna 8 da harsasai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!