Labarai
ASUU ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta biyansu albashin da suke bi tun 2022

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa ASUU, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta biyan membobinsu albashin watanni uku da ta rike musu tun a shekarar 2022.
Shugaban kungiyar reshen jami’ar Bayero da ke Kano Kwamred Yusuf Madugu, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da wakiliyarmu Halima Wada Sinkin.
Kwamared Yusuf Madugu ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayyar data cika musu dukkanin alkawuran data daukar musu kafin su yi yunkurin daukar Mataki a kai.
You must be logged in to post a comment Login