Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Atiku ya musanta ikrarin jami’yyar APC cewa bai cancanci tsayawa takara ba

Published

on

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar nan a tutar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya musanta ikirarin da jam’iyyar APC ta yi na cewa bai cancanci tsayawa takara ba sakamakon cewa ba a haifeshi a Najeriya ba.

Atiku Abubakar ya mai da martani ne kan korafin da lauyoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari suka shigar gaban kotun sauraran korafin zaben shugaban kasa.

A cewar Atiku Abubakar an haifeshi ne a ranar ashirin da biyar ga watan Nuwamban alif da dari tara da arba’in da shida a garin Jada da ke jihar Adamawa, a don haka shi dan Najeriya ne.

Tun farko dai jam’iyyar APC ta yi ikirarin cewa garin Jada wani bangare ne, na arewacin kasar kamaru a lokacin da aka haifi Atiku Abubakar.

A cewar sa, mahaifin sa Malam Garba Atiku Abdulkadir mutumin kasar Wurno ne da ke jihar Sokoto, yayin da mahaifiyar sa Aisha Kande mutumiyar Dutse ce da ke jihar Jigawa, kuma dukkannin su Fulani ne.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ci gaba da cewa, dalilin haifar sa da aka yi a garin Jada, ya samo asali ne sakamakon kaurar da kakar sa mai suna Atiku wanda bafatake ne yayi zuwa yankin na Jada tare da wani abokin shi mai suna Ardo Usman, inda a nan ne ma aka haifi mahaifin shi Garba.

Haka zalika dan takarar shugaban kasar karkashin jam’iyyar PDP ya ce a bangaren mahaifiyar sa, Aisha Kande, jikar Inuwa Dutse ne da ke jihar Jigawa a yanzu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!