Labarai
Atiku ya roki kotu kar ta hana shi takarar shugaban kasa a 2023
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma madugun jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, ya nemi babbar kotun tarayya da ke Abuja, da ta kori karar da aka shigar gabanta wadda ke bukatar hana shi takarar shugaban kasa a shekarar 2023.
Atiku wanda shine mutumin da ya yiwa jam’iyyar PDP takara a zaben shugaban kasa a shekarar 2019, ya ce, karar da wata kungiya mai suna Incorporated Trustees of Egalitarian Mission for Africa ta kai akansa ba ta da wata ma’ana.
A cikin takardar kalubalantar karar mai sadara 28 wadda wani mai suna Nanchang Ndam ya shigar a madadin tsohon mataimakin shugaban kasar, ta ce, babu abin da wadanda suka shigar da karar ke bukata face bata lokacin kotu.
Sauran wadanda kungiyar ta shigar da karar ta cikin takarda mai lamba FHC/ABJ/CS/177 ba ya ga Atiku Abubakar, sun hada da: Jam’iyyar PDP da hukumar zabe ta kasa INEC da kuma Atoni janar na tarayya kuma ministan shari’a.
Tun farko dai cikin takardar karar mai sadara 12 da wadanda ke kalubalantar Atiku Abubakar su ka shigar gaban kotu mai dauke da sa hannun wani mai suna Michael Okejimi, ta ce, Atiku Abubakar an haifeshi ne a ranar 25 ga watan Disamban 1946 a garin Jada da ke jihar Adamawa.
Saboda haka a cewar kungiyar Jada wani yanki ne a karamar hukumar Ganye, kuma garin na Ganye lokacin da aka haifi Atiku Abubakar ba yanki bane na Nigeria, a lokacin kasar Kamaru ne.
‘‘Ganye na cikin yankin kasar Kamaru da majalisar dinkin duniya ta mika kulawarsa karkashin Burtaniya bayan kammala yakin duniya na biyu a 1919 kafin daga bisani majalisar dinkin duniya ta karbe iko da yankin bayan kammala yakin duniya na biyu a 1946’’
‘’Yayin da Nigeria ta samu ‘yancin kai daga Burtaniya majalisar dinkin duniya ta tambayi yankin na Kamaru cewa ko yana son kasancewa a karkashin ikon Nigeria ko kuma hadewa da Kamaru’’
‘‘Har sai a ranar daya ga watan Yuni a 1961 arewacin Kamaru ya amince ya hade da Nigeria saboda haka a lokacin ne yankin Jada ya kasance a Nigeria, kuma kundin tsarin mulkin Nigeria ya ce sai wanda aka haifa a Nigeria ne kawai zai iya neman mukamin shugaban kasa’’ inji masu karar.
You must be logged in to post a comment Login