Labarai
Atiku:ya nemi kotu ta ayyana shi ya lashe zabe
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya nemi kotu ta ayyana shi ne ya lashe zaben bana da aka yi na ‘yan takarar shugaban kasa ko kuma a tsoke zaben gaba ki daya.
Atiku Abubakar wanda ya shigar da kara gaban kotu yana kalubalantar nasarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a babban zaben da aka yi na shugaban kasa dana ‘yan majalisar dokoki ta kasa a ranar 23 ga watan jiya.
A jiya Litinin ne Atiku Abubakar ya shigar da kara gaban kotun sauraran kararrakin zabe yana neman kotun ta ayyana shi ne ya samu nasara ko kuma kotun ta bada umarnin da a sake sabon zaben na shugaban kasa.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da cewar shugaban kasa Muhamamdu Buhari ne ya lashe zaben shugaban kasa, sai dai dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP yaki amincewa da sakamakon zaben, yayin da yayi zargin cewa an tafka kura-kurai.
Da yake ganawa da manema labarai mai baiwa jam’iyyar PDP shawara kan al’amuran shari’a Emmanuel Enoidem ya ce sun nemi kotun ta ayyana ‘yan takarar jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara a zaben wannan shekara ta 2019 da aka yi na shugaban kasa.