Ƙetare
AU ta dakatar da ƙasar Madagascar daga ƙungiyar

Tarayyar Afirka AU, ta dakatar da ƙasar Madagascar daga ƙungiyar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar Talata.
Hakan na zuwa ne bayan majalisar dokokin ƙasar ta tsige shugaba Andry Rajoelina bayan ya tsere daga ƙasar sanadiyyar ƙazancewar zanga-zanga.
Ba da daɗewa ba ne wata tawagar sojoji ta karɓe iko da ƙasar, inda ta yi alƙawarin gudanar da zaɓe cikin shekaru biyu.
Rahotonni sun bayyana cewa, zanga-zangar rikicin siyasa mafi muni da ta dabaibaye ƙasar cikin shekarun baya-bayan nan, bayan kwashe makonni ana zanga-zanga kan matsanancin ƙarancin lantarki da ruwa, inda masu zanga-zangar suka buƙaci shugaba Rajoelina ya sauka daga mulki.
You must be logged in to post a comment Login