Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Magoya bayan Buhari sun yi zanga-zangar goyon bayansa a birnin London

Published

on

Daruruwan magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari sun yi dafifi a ofishin diflomasiyar Najeriya da ke birnin London da akewa lakabi da Abuja House, don nuna goyon bayansu ga shugaban kasar da yaje birnin na London don ganin likita.

Rahotanni sun ce ‘yan Najeriyar mazauna London sun fito sun yi zanga-zangar ce don nuna goyon baya ga shugaban kasar tare da kalubalantar wasu ‘yan Najeriya da suka gudanar da zanga-zangar adawa da shugaban kasar a baya-bayan nan.

Bayanai sun ce, magoya bayan shugaban kasar sun yi ta daga kwalaye mai nuna alhini tare da addu’ar Alla.. ya bai wa shugaban kasar lafiya tare da yi masa addu’a na musamman don neman ubangiji ya bashi cikakken lafiya.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan biyo bayan zanga-zangar da Reno Omokri daya daga cikin masu taimakawa tsohon shugaban kasa Good luck Jonathan ya shirya wanda ke adawa da ziyarar London shugaba Buhari ke yi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!