Labarai
Ayyana ƴan takara da jam’iyyu ke yi a tsakiyar mulki ya saɓa dokokin zaɓe-INEC

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta ce ayyana ƴan takara da jam’iyyu ke yi tun a tsakiyar wa’adin mulki ya saɓa da dokokin zaɓe.
A cewar hukumar, kamata ya yi a bari masu mulki su sauke nauyin alƙawurran da suka ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓensu na baya, maimakon fara gangamin zabe na 2027 tun kafin lokaci yayi.
INEC, ta yi wannan jan hankalin ne bayan yawaitar al’amuran masu kama da yaƙin neman zaɓe a tsakanin jam’iyyu da kuma ƴan siyasar ƙasar, dake ciigba da wakana a fadin kasar.
Sanarwar ta INEC, wadda ta fitar a baya-bayan na zuwa ne biyo bayan yadda aka ga gwamnoni da ‘ƴan majalisa da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki a kasar suka sanar da cikakken goyon bayan su ga sake tsayawar shugaba Tinubu takara a zaɓe mai zuwa, da suka jaddada cewa babu wanda zai fito domin karawa da shi wajen neman kujerar a cikin jam’iyyar su.
You must be logged in to post a comment Login