Labarai
Ayyuka sun tsaya cak a Jami’ar Umaru Musa Yar’aduwa da ke Katsina

Hukumar gudanarwar Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina ta rufe makarantar bayan samun sabani tsakaninta da gwamnatin jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga batun albashin malamai da wasu bukatun da ma’aikata ke nema daga gwamnatin.
Wata sanarwa daga jami’ar ta tabbatar da cewa an dakatar da dukkan ayyukan karatu har sai an warware matsalar da ke tsakaninsu da gwamnatin jihar ta katsina.
You must be logged in to post a comment Login