Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Azal: Mutane 6 sun rasa ran su a hatsarin mota – FRSC

Published

on

Hukumar kiyaye abkuwar haddura ta kasa reshen jihar Bauchi ta ce mutane shida sun rasa rayukansu yayin da 54 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a jihar.

Kwamandan hukumar Yusuf Abdullahi ne ya tabbatar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai.

A cewar sa hatsarin ya rutsa da ’yan kasuwar da ke tafiya daga garin Darazo a karamar Hukumar Darazo da ke Jihar Bauchi zuwa Kasuwar Dakuku ta jihar Gombe.

Yusuf Abdullahi ya ce, a binciken su sun gano yadda motar mai dauke da fasinjoji 72 ke yin gudun wuce sa’a wanda hakan ne ya haddasa hatsarin, wanda kuma tuni an aike da wadanda suka jikkata zuwa asibiti don karbar kulawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!