Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Mun rufe gidajen mai a kano saboda kara farashin lita – DPR

Published

on

Sashin kula da Albarkatun Man Fetur na kasa DPR reshen jihar Kano, ya rufe wasu gidajen mai biyu a jihar sakamakon sayar da mai sama da farashin lita na naira dari da sittin da aka amince da shi.

Sashen ya kuma sanya takunkumi kan wasu gidajen mai takwas da aka gano sun boye shi.

Shugaban sashin gudanarwa da ke nan Kano Muhammad Makera ne ya sanar da hakan a jiya Laraba, jim kadan bayan kammala zagayen duban yadda gidajen mai ke ci gaba da kasuwancin su don sanya ido kan aiwatar da farashin da aka sanya.

A cewar sa gidajen man da aka rufe da wadanda aka sanyawa takunkumi sun karya ka’idojin da aka gindaya.

Muhammad Makera ya tabbatar da cewa za a dauki kwakwaran mataki ga duk wanda ya karya ka’ida na sayar da litar mai a kan kudi sama da naira dari da sittin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!