Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Azumi: Ganduje ya umarci ƴan KAROTA su sassauta wa jama’a

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bai wa hukumar KAROTA umarnin su sassauta wa al’umma a lokacin watan azumi.

Shugaban hukumar Baffa Babba Ɗanagundi ne ya bayyana hakan a zantawar sa kai tsaye da Freedom Radio ta cikin labaran Mu Leƙa Mu Gano na ranar Asabar.

Baffan ya ce, Gwamna ya basu umarni su ɗaga ƙafa ga al’umma saboda zuwan wata mai alfarma.

A saboda haka jami’an za su mayar da hankali ga aikin hukumar kare haƙƙin masu saye domin bankaɗo masu cutar da jama’ar jihar Kano.

“Zamu jingine ayyukan KAROTA gaba ɗaya kamar yadda mai girma Gwamna ya yi umarni a watan azumi, domin mu ƙara bankaɗo masu sayarwa da jama’a gurɓatattun kaya” inji Baffa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!