Connect with us

Labaran Kano

Ba Amurkiya daga California ta biyo saurayinta zuwa Kano

Published

on

Wata ba amurkiya da ke zaune a birnin carlifonia tayo tattaki daga Amurkan bata zame ko in aba sai a unguwar Panshekara dake nan Kano, tazo takanas ta Kano domin ganawa da wani saurayin ta, dan Kano mazaunin Panshekara wanda su ka kulla abota a dandalin sada zumunta daga bisani kuma abin ya zama soyayya me karfi har takai guda baya iya runtsawa sai ya ji muryar gudan.

Tafiya dai ta yi dole karshe Baturiya Janet ta ga cewar ai gara ayi ta dungurum gum haihuwa da hanji, dan haka ta yanki tikiti ta hawo jirgi ta sauka a Panshekara, ta kuma shiga har cikin gidansu wannan saurayi na ta Suleman wanda ta ce ya gama sace zuciyar ta da kalamai na soyayya da hotunan qawa da ya ke tura mata cikin yanayin rangwada, ta kuma yi mana Karin hasken cewar, ta shirya tsaf domin daukar wannan saurayi nata domin tafiya dashi amurka a cigaba da soyewa

Suleman shi ne saurayin da tarkon sa ya kama kucciya, har takai an yo masa takakkiya daga carlfonia,zuwa gidan su dake panshekara, ya ce shima fa ya yi mata kuma kayansa su na jaka zai bi matar ta sa amma ya yi alkwarin zai dinga kawo ziyara gida

Itama Fatima Suleman mahaifiyar wannan saurayi da makota ke yiwa barka ta ce, bata da suka kan wananan alaka dan haka a tafi amurka ta amince, tun taga ita baturiyar bin tun jamilatun ce

Wani abu da shima ke jan hankali shi ne ita fa wannan ba Amurkiya shekarar ta 46 shi kuwa Suleman yaro ne sharaf mai shekaru 23,ko yaya auran zai yiwu tsakanin sa da old woman, zamu ji amsa a shirin mu na gaba.

Ku biyo cikin shirin Inda ranka don jin cikakken labarin

 

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!