Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ba don a bani takarda nake Kwankwasiyya ba – Nadiya Fagge

Published

on

Fitacciyar ƴar Kwankwasiyyar nan Nadiya Ibrahim Fagge ta magantu kan rashin bata takardar neman goyon baya daga Abba Gida-gida.

A baya-bayan nan ne dai Ɗan takarar Gwamnan Kano a NNPP Abba Gida-gida ya aike da takardar ga wasu fitattun mutane a Kano.

A cikin takardar ya sanar da su takararsa tare da neman gudunmawarsu.

Cikin waɗanda Abban ya aike wa takarda har da matashiyar nan ƴar gwagwarmaya Zainab Nasir Ahmad.

Sai dai hakan ya haifar da kace nace.
Ga ƙarin bayani kan wannan

A saƙon da ta wallafa a shafinta na Facebook ta bayyana yadda jama’a suka riƙa tagging ɗinta kan batun bai wa Zainab takardar.

Sai dai Nadiyan ta nuna cewa ita Kwankwaso zalla take yi ba don takarda ko kuɗi ba sai don aƙida.

Ta ce, duk inda Kwankwaso ya nuna nan ne alƙiblarta.

Dangane da Zainab kuwa Nadiya ta ce, ta san ba za a bai wa Zainabun takarda kan bai wa Kwankwasiyya gudunmuwa ba, a’a sai dai ko don a yaba mata ta wani wajen.

Nadiya ta ci gaba da cewa, masoyanta su daina damuwa don ba a bata takarda ba.

Ta ce, “Allah shi ne shaida ba saboda wani muƙami ko abin duniya nake yi ba, shi yasa na zama ƴar siyasa mai zaman kanta, ina sana’a kuma ina aiki”.

“Kuma Alhamdulillah sun rufa min asiri ban taɓa maula wajen wani ɗan siyasa ba, wannan ma kaɗai ni’ima ce Allah ya yi min” in ji Nadiya

A ƙarshe Fagge ta rufe da cewar “Abu ɗaya na sani, kuma na tsaya a kai a harkar siyasa, bana zuwa inda ba a gayyace ni ba, ko ba a san ƙimata ba”.

Meye ra’ayinku a kai?

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!