Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ana kace-nace kan takardar Abba Gida-gida ga Zainab Nasir

Published

on

Zainab Nasir Ahmad, Abba Gida Gida

Cece-kuce ya ɓarke a kafafen sada zumunta kan takardar neman goyon baya da ɗan takarar Gwamnan Kano a jam’iyyar NNPP ya aike wa matashiyar nan Ƴar Gwagwarmaya Zainab Nasir Ahmad.

Matashiyar wadda ita ce shugabar ƙungiyar matasa, mai yaƙi da cutuka da mugayen ɗabi’u ta YOSPIS ta bayyana farin cikinta kan takardar.

Sai dai da alama wannan takardar bata yiwa wasu mabiyan Kwankwasiyya daɗi ba, inda suka shiga bayyana ra’ayoyinsu a kai.

Haka ma wasu da ba ƴan Kwankwasiyyar ba, sun shiga yin tsokaci kan lamarin.

Ga wasu daga ciki da muka tsakuro muku.
Tuni dai Kakakin Ɗan Takarar Gwamnan na NNPP Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya tsawatarwa da ƴan Kwankwasiyyar da ke guna-guni kan wannan takarda ta Zainab.

A saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce, ba Zainab kaɗai aka aike wa wannan takardar ba, har da masu ruwa da tsaki daga ɓangarori daban-daban.

Ku meye ra’ayinku a kai? 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!