Labarai
Ba gudu ba ja da baya kan batun yajin aiki – JOHESU

Gamayyar kungiyoyin Ma’aikatan lafiya ta ta kasa ta bukaci mambobinta dasu cigaba da gudanar da yajin aiki sai baba ta gani duk da matakin gwamnatin tarayya na babu aiki babu Albashi.
Hakan na cikin wata sanarwa da Sakataren Kungiyar na Kasa, Mista Martin Egbanubi ya sanya wa hannu, kuma aka aika wa shugabannin kungiyoyin kwadago na jihohi.
cewar ƙungiyar, cigaba da yajin aikin biyo bayan ƙudurorin da shugabanninta na ƙasa suka cimma a wani taron gaggawa na intanet da aka gudanar don yin bitar abubuwan da suka faru.
You must be logged in to post a comment Login