Labarai
Ba ma bukatar rancen kudi na TISSF- ASUU

Ƙungiyar Malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU, ta bayyana ƙin amincewarta da sabon shirin da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar na bayar da lamunin kuɗi ga ma’aikatan jami’o’i, na Tertiary Institutions Staff Support Fund TISSF.
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Christopher Piwuna, ya bayyana cewa membobin ASUU ba sa buƙatar wannan bashi, illa dai a inganta albashi da yanayin aiki.
ASUU ta yi gargadi cewa tsarin aron zai ƙara matsaloli ga malamai, musamman ganin yadda ake riga da cire kuɗaɗen fansho, lafiya da kuma na ƙungiyoyi daga albashin su. Ƙungiyar ta ce wannan zai iya lalata harkokin haɗin gwiwar ƙungiyoyi da malamai ke dogaro da su.
Kungiyar ta kuma sanar da shirinta na gudanar da zanga-zangar gargadi a jami’o’i a mako mai zuwa, tare da jan kunne cewa idan gwamnati ba ta ɗauki matakin da ya dace ba a taron da aka shirya yi a ranar 28 ga Agusta, 2025, to za a iya shiga sabon yajin aiki.
You must be logged in to post a comment Login