Labarai
Ba ma goyon bayan rukunin rabon makamashin Lantarki Engr. Sani Bala Tsanyawa

Majalisar wakilan Najeiya, ta ce, ba ta goyon bayan yadda ake rarraba wutar lanatarki a tsakanin ga mutane da kuma kamfanoni.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Ghari da Tsanyawa a majalisar dokokin kuma Mamba a kwamitin wutar lantarki na majalisar Injiniya Sani Bala Tsanyawa, ne ya bayyana hakan a ganawarsa da Freedom Radio a yau Litinin.
Injiniya Sani Bala Tsanyawa ya kuma ce majalisar za ta kara gayyatar ministan makamashin lantarki domin janye tsarin da ake amfani da shi a yanzu na bayar da wutar a mabanbanta rukuni na Band A da B da Kuma C.
You must be logged in to post a comment Login