Labarai
Matsalolin kiwon kifi a Najeriya
ƙungiyar masu kiwon kifi ta ƙasa rashen jihar Kano ta ce babban kalubale da ta ke fuskanta bai wuce rashin samun abincin kifi da aka sarrafa a kasar nan ba.
Sakataren ƙungiyar Maharazu Usman ne ya bayyana haka yayin tattaunawa da Freedom radiyo.
Ya ce kamata yayi ace gwamnatin tarayya ta bada goyon baya wajen yiwa matasa horo kan yadda za su sarrafa abincin kifi a ƙasar nan.
Ya kara da cewa “ Idan muka yi duba da yadda gwamnatin ke son a daina shigo da kifi kamata yayi ace a yanzu ana sarrafa abincin kifin a kasar domin a habaka harkar sana’ar kifi da kiwon ta”.
Kazalika ya koka kan yadda rashin abincin ke kawo musu koma baya a harkokin kiwon kifin.
You must be logged in to post a comment Login