Labarai
Ba mu da hannu wajen sayar da Injin Ban Ruwa- Gwamnatin Kano
Gwamnatin Jihar Kano, ta musanta labaran da ke yawo cewar da sanin ta aka yi yunkurin cefanar da wani injin Ban ruwa dake garin Karefa a karamar hukumar Tudun Wada.
Kwamishinan ma’aikatar Ruwa ta jihar Ali Haruna Makoda wanda ya samu wakilicin Darakatna sashin kula da Noman rani da madastun ruwa na ma’aikatar Adamu Chiroma, ne ya musanta batun yana mai cewa, ko kadan babu sani shugabannnin ma’aikatar kan wannan aika-aika.
Ya kuma kara da cewa Daraktan mulki na ma’aikatar shi ne ya hada kai da wasu gurbatattun mutane, inda suka rubuta takarda da sunan Kwamshinan Ruwa ne ya bada umarnin a cire injin.
Adamu Chiroma ya kuma ce tuni wadannan mutane suka shiga hannun hukuma bayan da masu kula da Injin suka sanar da Kwamishina halin da ake ciki.
Yanzu haka dai mutanen da ake zargi da yunkurin cefanar da injin sun tabbatar da cewa babu sanin shugabannin ma’aikatar Ruwa a yunkurin da sukai na cefanar injin, kamar yadda suka shaida bayan sun shiga hannun rundunar yan sanda jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login