Labaran Kano
Ba mu da shirin tafiya yajin aiki – IPMAN
Kungiyar dillalan man fetur ta kasa, IPMAN, shiyyar jihar Kano, ta ce bata da shirin tafiya yajin aiki saboda karin kudin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi cikin makon jiya.
Shugaban kungiyar, shiyyar Kano, Alhaji Bashir Dan-Malam ne ya bayyana haka a ranar Litinin, jim kadan bayan kammala shirin ‘Barka da Hantsi na nan tashar Freedom Rediyo da ya maida hankali kan karin farashin man fetur zuwa Naira 145 kowace lita daya.
Alhaji Bashir Dan-Malam ya ce karin kudin man fetur din da gwamnati tayi ba zai rasa nasaba da yadda aka samu karin yawan man a kasuwar duniya ba.
Labarai masu alaka:
Al’umma su kwantar da hankulan su-IPMAN
Gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti nazarin matsalar karancin man fetur
Shugaban IPMAN ya kara da cewa duk lokacin da aka samu man gwamnati na kara firiashin don radin kanta, a don haka ya yi kira ga abokan huldarsu da su fahimci cewa karin ba daga wajensu yake ba.
Dan-Malam ya yi fatan karin da aka yi na kwanan nan ba zai jawo wata matsala ba a bangaren gudanar da al’amuran yau da kullum na jama’a ba.
You must be logged in to post a comment Login