Labarai
Ba mu fara ɗaukar sabbin ƴan sanda ba – Maigari Dingyadi
Ma’aikatar harkokin ‘yan sanda ta tarayya ta gargadi ‘yan Najeriya da su yi watsi da rahoton da ke yawo a shafukan sada zumunta cewa za a dauki sabbin ‘yan sanda dubu 400.
Ministan ma’aikatar Alhaji Muhammad Dingyadi ne ya yi wannan gargadi ta cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran ma’aikatar Osaigbovo Ehisienmen ya fitar jiya a Abuja.
Muhammad Dingyadi ya ce, wasu bata-gari ne ke yada labaran bogi domin damfarar al’umma da ke neman aikin.
A don haka ya shawarci jama’a da su kaucewa fadawa tarkon ‘yan damfara, har ma ya ce tun a shekarar 2019 ne gwamnatin tarayya ta ba da umarnin daukar kuratan ‘yan sanda dubu arba’in, kuma tuni aka dauki dubu goma a matakin farko.
You must be logged in to post a comment Login