Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za’a kara daukar sabbin ‘yan sanda :Gwamnati

Published

on

Shugaban hukumar kula  da harkokin ‘yan sanda ta kasa Muhammad Dingyadi ya ce nan gaba kadan gwamnatin tarayya za ta sake daukar sababbin kuratan ‘yan sanda su dubu goma.

Muhamma Dingyadi ya ce sake daukar kuratan ‘yan sandan su dubu goma na cikin shirin nan na shugaban kasa Muhammadu Buhari na daukar Yansanda dubun  arabain a fadin kasara nan.

Rundunar ‘yan sanda ta Kano zata daura dammara wajen yaki da shaye-shaye

‘Yan sanda sun baiwa ‘yan social media horo na musamman

Masu kwacen waya sun zo hannu -‘Yan sanda

Shugaban ya bayyana hakan ne a birnin Abuja lokacin kaddamar da wani littafi mai taken Introduction to Law Enforcement wanda wani tsohon babban mukaddashin Sufeto Janar na ‘Yan sandan kasar nan Adeyemi Ogunjemilusi ya rubuta.

Muhammad Dingaydi ya ce ana nan ana shirya yadda za’a dauki ‘yan sandan domin kara yawansu a fadin tarayyar kasar nan da kuma maganin rashin tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!