Labarai
Ba mu kori ko mutum guda daga ma’aikatan mu ba -NEMA
Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta musanta rahotannin da ke cewa ta kori wasu ma’aikatanta guda arba’in da takwas.
Mai magana da yawun hukumar Manzo Ezikiel ta cikin wata sanarwar ya ce babu kanshin gaskiya cikin batun.
Tun farko dai kafafen yada labaran kasar nan sun ruwaito cewa hukumar ta NEMA ta kori ma’aikatanta guda arba’in da takwas wadanda ta daukesu aiki a shekarar da ta gabata.
You must be logged in to post a comment Login