Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kungiyar manyan ma’aikatan lantarki na kasa da na KEDCO sun tsunduma yajin aiki

Published

on

Kungiyar manyan ma’aikatan bangaren wutar lantarki da takwarorinsu na kasa sun tsunduma yajin aiki tare da garkame babban ofishin kamfanin rarraba wutar lantarki shiyyar Kano KEDCO a safiyar yau.

 

Dubban ma’aikatan kamfanin dai sun yi cincirindo a kofar ofishin bayan da aka garkame shi tun da sanyin safiya.

 

Tun da fari an gudanar zanga-zangar kin nuna goyon baya da dumbin ma’aikatan kamfanin suka yi  bisa ga halin da su ke ciki na rashin kyautatawar da suka ce kamfanin na yi musu.

 

Dalilan da ya sanya suka tsunduma yajin aikin:

 

Cikin dalilan da suka sanya su yajin aikin a cewar Sakataren kungiyar manyan ma’aikatar wutar lantarki ta kasa yankin Arewacin kasar nan, Kwamred Raji Ahmad Rufa’i sun hada da: “gaza biyan su Albashi na tsawon wata 13, da zabtare musu kudaden Fansho da rashin kayan aiki da Kuma tura su wajen aiki ba bisa ka’ida ba a duk lokacin da kamfanin ya ga dama”

 

Sai dai a gefe guda Shugaban Kungiyar Kwadago ta kasa reshen Jihar Kano, Kwamred Kabiru Ado Minjibir yace kungiyar ba zata Lamunci halin da ma’aikatan kamfanin ke ciki ba, don haka za su dauki dukkanin matakan da suka kamata tare da nuna goyon baya.

 

Sai dai har yanzu kamfanin na KEDCO bai bai yi karin haske kan lamarin ba, inda mai magana da yawun kamfanin Ibrahim Sani Shawai ya ce suna kan tattaunawa da shugabannin kamfanin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!