Labarai
Ba mu shirya janye yajin aiki yanzu ba – ASUU
Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU ta musanta labarin cewa za ta janye yajin aikin da take yi nan ba da jimawa ba.
Shugaban ƙungiyar mai kula da shiyyar Kano Farfesa Abdulƙadir Muhammad ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.
“Ba mu da wani shiri na janye yajin aiki yanzu, hasalima babu wani taron tattaunawa da muke yi a halin yanzu”.
Ya ci gaba da cewa “Muna da tsari na sanar da abubuwan da muke aiwatarwa, ya kamata mutane su sane akwai matakai da muke bi wajen sanar da yajin aiki, don haka wannan labari kanzon kurege ne”.
“Mambonin mu sun ba mu umarnin cewa kada ma ayi tunanin za a kira su a nemi shawarar su har sai gwamnati ta kira su ta biya musu buƙatunsu, wanda kuma har yanzu gwamnatin bata da wani yunkuri na yin hakan”.
A ɗazu-ɗazun nan ne dai wata jaridar Internet mai suna DAILY POST ta rawaito cewa, kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU za su janye yajin aikin da suka shafe watanni uku suna yi nan ba da jimawa ba.
You must be logged in to post a comment Login