Connect with us

Coronavirus

Corona ta sake bulla a jihar Zamfara

Published

on

Gwammatin jihar Kano ta tabbatar da cewar an samu karin mutum 9 dauke da cutar Corona a jihar, cikin mutane 422 da aka yiwa gwajin cutar a ranar Asabar.

Ma’aikatar lafiya ta Kano ce ta sanar da hakan a shafinta na Twitter, inda ta ce zuwa yanzu adadin wadanda suka kamu da cutar Corona a jihar sun kai 1,395.

Mutum 1,100 daga ciki sun warke, sai 53 da suka rigamu gidan gaskiya sanadiyyar cutar.

Ya zuwa yanzu masu cutar ta Covid-19 mutum 242 ne ke ci gaba da jinyar cutar a Kano.

A wani labarin kuma, cibiyar dakile bazuwar cutuka ta kasa NCDC tace a ranar Asabar an gano mutum 653 dake dauke da cutar Corona a jihohi 28 da babban birnin tarayya Abuja.

Daga cikin jihohin da aka samu karin masu cutar a jiya Asabar, har da jihar Zamfara wadda aka samu karin mutum guda, bayan da jihar ta shafe kwanaki sama da 50 ba tare da an samu bullar cutar ba.

NCDC ta sanar a shafinta na Twitter cewa adadin masu cutar Corona a Najeriya ya kai 36,107.

14,938 daga ciki sun warke, sai mutum 778 da cutar tayi ajalin su a Najeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,993 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!