Connect with us

Labarai

Ba ni da wani shiri na musanya wasu jami’an KAROTA – Inji Baffa Babba

Published

on

Hukumar lura da zirga-zirgar ababan hawa ta Kano KAROTA ta yi martani kan wasu zarge-zarge da wasu cikin jami’an hukumar suka yi.

Jami’an dai sun zargi cewa shugaban hukumar na horar da wasu matasa a kwalejin Rumfa waɗanda ake sa ran za su maye gurbin wasu ma’aikatan hukumar ba tare da wani dalili ba a cewar su.

Sun kuma zargi cewa, an yanke wa da yawa daga jami’an hukumar albashi a watan da ya gabata, a don haka su ke neman majalisar dokokin Kano da hukumar ƙarɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar Kano, da kwamishinan kuɗi kan su shiga lamarin domin kawo daidaito.

To kan waɗannan ƙorafe-ƙorafe wakilinmu Yusuf Ali Abdallah ya tuntuɓi Baffa Babba Ɗanagundi wanda ya ce babu gaskiya cikin iƙrarin na su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,845 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!