Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

A shirye nake na bayyana a gaban kotu – Baffa Babba

Published

on

Shugaban hukumar lura da zirga-zirgar ababan hawa ta Kano KAROTA Baffa Babba Ɗanagundi ya ce a shirye yake ya bayyana a gaban kotu.

Cikin wani jawabi da Baffa Babba ya fitar a baya-bayan nan ya ce yana so ya rinƙa girmama kotu, domin al’ummar gari su san cewa babu wani jami’in gwamnati da ya fi ƙarfin doka.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Baffa Babban ya ƙaurace wa zaman kotun majistare da ke Gidan Murtala a nan Kano, wadda ta umarce shi da ya bayyana a gabanta bisa ƙarar da wani direban adaidata sahu ya shigar game zargin zamba cikin aminci.

Kotun ta sake sanya ranar 19 ga watan Oktoban da muke ciki kan lallai ya bayyana a gabanta ko kuma ta ɗauki mataki a kansa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!