Connect with us

Labarai

Ba ni ne nake bincikar Bola Tinubu ba – Malami

Published

on

Ministan shari’a kuma Atoni Janar na tarayya Abubakar Malami ya musanta cewa yana bincikar jagoran jam’iyyar APC na kasa Bola Ahmad Tinubu.

Abubakar Malami ya yi wannan jawabi ne a wata tattaunawa da gidan Talabijin na Channels.

“To amma babu wani karin haske da zan iya yi kan ko Tinubun yana fuskantar tuhuma daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ko hukumar kula da da’ar ma’aikata, kasancewar hukumomin biyu na da hurumin bincikar kowa tare da gurfanarwa a gaban Kotu” in ji Malami.

”Kamar yadda aka sani, babu wani mataki ko kuma korafi da ofishi na ya shigar gaban Kotu, game da wasu kadarori da ake dangantawa da Bola Tinubu” a cewar ministan.

A ranar 20 ga watan Nuwamban bara ne dai EFCC ta aikewa hukumar kula da da’ar ma’aikata wasika da ke bukatar cikakkun bayanai kan kadarorin da Bola Ahmad Tinubu ya mallaka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!