Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za a hukunta jami’an KAROTA kan cin zarafi

Published

on

Hukumar KAROTA ta ce, za ta hukunta wasu jami’an ta da suka ci zarafin wani matashi a ranar Talata 09-03-2021.

A cikin wata sanarwar da jami’in yaɗa labaran hukumar Nabulisi Abubakar Ƙofar Na’isa ya fitar a ranar Laraba ya ce, sun shiga bincike kan lamarin.

A cewar sa, sun lura da wani bidiyo da ke yawo a gari na bidiyon jami’an ta da matashin.

A cikin bidiyon dai an hangi yadda jami’an KAROTAr suka shaƙe wuyan matashin tare da zagin sa.

Ku kalli bidiyon a nan

Hukumar KAROTA ta ce, an kama matashin ne bisa zargin yin waya a lokacin da yake tuƙa babur mai ƙafa biyu a titin zuwa filin jirgin saman Kano.

KAROTA ta ci gaba da cewa, waɗannan jami’an na ta sun saɓa wa doka, kuma sun yi aiki cikin rashin ƙwarewa.

Tuni shugaban hukumar Baffa Babba Ɗanagundi ya bayar da umarnin zurfafa bincike domin ɗaukar mataki a kan jami’an.

A ƙarshe Baffa Babba ya roƙi jama’a kan su ci gaba bai wa hukumar haɗin kai wajen bin dokokin tuƙi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!