Labarai
Ba za a ga ci gaba a ƙananan hukumomi ba, har sai an bamu ƴancin cin gashin kai – Tambai Ƙwa
Shugaban karamar hukumar dawakin Tofa anan Kano Alhaji Ado Tambai Ƙwa ya ce, matukar ana son kananan hukumomi su ci gashin kan su, ya zama wajibi a gyara kundin tsarin mulkin ƙasar nan.
A cewar sa rashin bai wa kananan hukumomin ƴancin cin gashin kai, na taka rawa wajen hana yin ayyukan ci gaban al’umma a kananan hukumomi.
Alhaji Ado Tambai Ƙwa ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin “Barka da hantsi” na nan tashar Freedom radio, da shirin ya mayar da hankali kan rashin barin kananan hukumomi su ci gashin kan su.
“Idan har ana so mu kawowa al’ummar da muke mulka ci gaba, to kuwa akwai bukatar a sake nazari a kundin tsarin mulkin ƙasar nan, don yin waiwaye ga me da batun bai wa kananan hukumomi ƴancin cin gashin kai” a cewar Tambai Ƙwa.
Ya ce, idan har za a bar kananan hukumomi su ci gashin kan su, to kuwa da an samu ci gaban da ake buƙata, kasancewar su ne suka san irin abubuwan da al’ummar su ke bukata.
You must be logged in to post a comment Login