Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Eid-el-kabir: Akwai yiwuwar barkewar cutar Corona samfurin Delta a Kano

Published

on

Gwamnatin tarayya ta gargadi jihohi shida na kasar nan kan barazanar sake bullar annobar Corona karo na uku samfurin Delta.

Jihohin da ake farbagar barkewar cutar sun hadar da: Lagos, Oyo, Rivers, Plateau, Kaduna da kuma Kano.

Kwamitin da ke yaƙi da cutar Corona na shugaban kasa ne ya fitar da gargadin, cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya sanyawa hannu.

Kazalika kwamitin ya bukaci ‘yan Najeriya da su kara lura da matakan kariya daga cutar, yayin bukukuwan sallah babba don kiyaye yaduwarta a tsakanin al’umma.

Kwamitin ya shawarci da a dakatar da hawan sallah na al’ada, da kuma samar da matakan kare yaduwar ta a wajen sallar idi.

Idan za a iya yunawa, tun a ranar 8 ga watan Yuli ne cibiyar NCDC ta bayyana cewa, ta gano nau’in kwayar cutar Corona samfurin Delta mai saurin yaduwa tsakanin alumma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!