Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘yan ta’adda su watsar da makamai su rungumi tsarin zaman lafiya – Sojoji

Published

on

Rundunar sojin Najeriya ta bukaci ragowar ‘yan ta’addar Boko Haram da su mika wuya tare da rungumar tsarin zaman lafiya.

Babban kwamandan runduna ta 7 ta sojojin Nijeriya, Birgediya janar A.A. Eyitayo, ya yi kiran ne a wajen wani biki da sojoji suka shirya wa ‘yan jarida a Lahadin nan a Maiduguri.

Eyitayo, wanda kuma shi ne Kwamandan shiyya ta 1 ta Operation Hadin Kai, ya ce harin da sojoji suke kai wa a kan ‘yan ta’adda suna matukar samun nasara a kan su tare da sanya ragowar cikin rudani.

Eyitayo ya yaba da gudummawar da kafafen yada labarai ke bayarwa wajen yaki da masu tayar da kayar baya, inda ya bukace su da su ci gaba da bada gudunwa ta hanyoyin da suka dace don samun nasara a kan mayakan na Boko Haram, wajen zubar da makaman su domin kuwa da yawan su suna sauraron kafafen yada labarai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!