Labarai
Ba za mu amsa gayyatar majalisa ba- Gwamnonin Zamfara da Benue

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare da takwaransa na Benue Hyacinth Alia, sun ce ba za su amsa gayyatar da Kwamitin karɓar ƙorafe-ƙorafe na Majalisar Wakilai ya yi musu ba, sakamakon shakku kan halaccin gayyatar.
A baya dai Majalisar ta gayyaci gwamnonin da majalisun dokokin jihohin su ne domin su bayyana a gaban kwamitin bisa zargin saba kundin tsarin mulki da gazawa wajen gudanar da mulki, da kuma fama da matsalar tsaro da rikici tsakanin wasu ‘yan majalisar dokokin jihohin.
Gayyatar na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban kwamitin yada labarai da korafe-korafe na majalisar wakilan, Chooks Oko, ya fitar ranar Juma’ar da ta gabata.
Haka kuma gayyatar ta bukaci sanin ko suna da ja kan kudurin majalisar wakilan na karbe ikon gudanar da ayyukan majalisun jihohin biyu, kamar yadda sanarwar ta ce sashe na 11, (4) cikin Baka na kundin tsarin mulkin kasar na 1999 ya bayar da dama.
Sai dai, a jihar Benue, akwai takaddamar dakatar da wasu ‘yan majalisar jihar 13, wadanda ba sa jituwa da gwamnan jihar, yayinda a jihar Zamfara aka samu majalisa biyu, inda wasu ‘yanmajalisa tara suke ikirarin damar ci gaba da aikinsu duk da cewa an dakatar da su.
You must be logged in to post a comment Login