Labarai
Ba za mu biya ma’aikata albashin Afrilu ta banki ba- Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce, ba za ta biya ma’aikatanta albashin watan nan da muke ciki na Afrilu ta hanyar banki ba, maimakon haka za a biya su ne kai tsaye ta hanyar tantance su a hukumomin da su ke aiki.
Sakataren gwammatin Kano Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai dangane da gano ma’aikatan kananan hukumomi sama da dari biyu da suka bar aiki wasun su suka rasu amma ana ci gaba da biyan albashi a asusun su.
Alhaji Umar Faruk Ibrahim ya ce, gwamnati za ta gayyaci ma’aikatan da aka gano suna karbar albashi sau biyu a ma’aikatar da suke aiki don yin bayani.
Haka kuma Sakataren gwamnatin ya ce, gwamnati za ta magance yadda ake bai wa ma’aikata bashin kaya sakamakon gano yadda ake cutar da su a fannin.
You must be logged in to post a comment Login