Connect with us

Coronavirus

Ba za mu bude makarantu ba a halin yanzu – Minista

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce, har yanzu ba ta tsayar da lokacin da za a bude makarantu kasar nan.

Karamin minstan ilimi Mr Chukwuemeka Nwajuba ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke gabatar da jawabi ga kwamitin karta kwana na gwamnatin tarayya kan yaki da cutar corona jiya a Abuja.

Ya ce, har yanzu dai maganar komawa makarantun kasar nan ba a cimma matsaya ba sai dai ana ci gaba da tattara bayani.
A cewar ministan gwamnati tarraya na ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki musamman na manyan makarantun kasar nan don samar da mafita, yana mai cewa.

Yana mai cewa, wasu manyan makarantu masu zaman kansu suka bukaci da a basu damar ci gaba da karatu sai dai gwamnatin na son tabbatar da adalci ga dalibai baki daya wanda ya sanya bata basu dama ba.

Nwajuba ta cikin jawabin nasa ya bukaci dalibai da su kara hakuri tare da nazartar karatukan da aka yi musu na baya don bunkasa ilimin su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!