Connect with us

Labarai

Ba za mu dawo da ƴan sandan SARS ba – IG Alƙali Baba

Published

on

Babban sufeton ‘yan sandan ƙasar nan Usman Alƙali Baba, ya ce rundunar ba ta da wani shiri na sake dawo da ‘yan sandan yaki da manyan laifuka na fashi da makami da shugaban ƙasa ya rushe wato SARS.

Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Frank Mba ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Frank Mba ya ce sanarwar ta biyo bayan yadda wasu kafofin yada labarai ke yaɗa rahoton cewa babban sufeton ‘yan sanda ya ba da umarnin sake dawo da ‘yan sandan na SARS.

Ya kara da cewa tun bayan rushe ‘yan sandan SARS din ne rundunar ta samar da tsarin cike gibinsu, domin ci gaba da aikin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Najeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!